ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng Abin ya baiwa Surajo dariya, in wani ne ya bashi labarin Abubakar Mukhtar (sunan da suke kiranshi) zai koma haka akan mace karyatawa zai yi. Soyayya ba karya bace, a yau ya kara yarda da hakan. Ya shiga girgida kai kamar kadangare. “Tana ina ne? Ban ji motsinta ba. Ga hotunan (cocktail) din ku fa na wanko”. Ya amsa ya aje gefe ba tare da ya bude ba yayi mai nuni da (kitchen) da girar shi. Dariya Surajo yayi, “Kace har girki ake mana!”. Shima dariyar yayi, “Mai dadi kuwa”. Suka yi ta dariya kamar wasu shashashan madina, sai da suka yi mai isarsu tukunna. Surajo ya ce, “To yanzu yaya za’ayi batun tafiya UK?” “Sai yanda ta yiwu Surajo, bani da sauran dabara, duk abinda zan iya nayi, na bada hakuri, nayi fada, nayi wa’azi, nayi nasiha. Zan iya cewa (there are lots of improvements) sai dai bata yi min magana, sannan in nayi bata amsa min da baki, sai dai tayi a aikace. Kuma ba musu, ba rashin kuny…