ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng Washegari da safe, mun karya kumallo cikin farin ciki, ni Ummi da ragowar kannen mu. Daga nan muka tare a falon Ummi muna hira muna shan dariya. Na mike na barsu nayi (toilet) din Ummi nayi wanka na sha kwalliya da daya daga cikin lesukan Ummi da ta ci biki dasu. Na dawo falon na cimma su kafin in zauna kararrawar kofar shigowa tayi kara. Sai na fasa zama a raina na ce bari in hutar da kowa. Na karasa a natse na bude kofar. Fa’iz ne cikin shadda wagambari babbar, ruwan makuba tare da abokinsa Surajo na Central Bank, shi kuwa cikin kananan kaya. Da ganinsu kaga matasan da rayuwa ke garawa tare dasu, suna cikin lokacinsu, kuma ana damawa dasu a fannonin da suke. Muka hada ido da Fa’iz na yi maza na kawar da nawa na wuce ciki na zauna kusa da Ummi ban kara kallon su ba. Na kuma bi na maida fuskata kamar hadari sai ka rantse ba dani ake hira da dariya yanzun nan ba. Su Ummi s…