ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER  8 by Sumayyah Abdul-kadir                   Www.bankinhausanovels.com.ng  iyaye da ‘yan uwana.  Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce.  “Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama”.  Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba. A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa’iz tafi dubu biyar.  Na rame, na fige, na zama ‘yar firit dama jikin ba wani jiki ba. Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba. Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni. Ko babu komi ranar da Fa’izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa? Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan.  Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai…