ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng  anyita ba dadi da Fa’izah. Hasashen shi ya hasaso mishi ita ce ta yiwa Fa’iz wannan raunin.  Fa’iz ya ja numfashi ya sauke, da gasken-gaske cikin damuwa yake mai yawa, wadda ta kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar shi.  Maajid ya bubbugi kafadunshi, ya yi murmushi ya ce.  “WO-MAN! Inka fahimci kalmar ko? Tana nufin Wo! MAN ka shiga uku kenan!””.  Duk halin da Fa’iz yake ciki sai da Maajid yasa shi dariya, ya yi mai isarsa kafin ya ce.  “Maajid! Maajid!! Ya aka yi kasan cewa Fa’izah ce ta rotsa ni?”  Ya ce, “Oho maka wannan kuma! Ni dai na san kai ba makaho bane balle ince faduwa kayi ka ci da baka ka fasa goshi ka fasa kai, na kuma san ba dambe kayi ba aka fi karfinka da (giantness) din nan naka Fa’iz. Na kuma tabbata ba gidan giya kaje wani yasha ya bugu ku kayi rigima ya rotsa maka kwalbar ba”.  Sai ya sake tintsirewa da dariya, ya ce.  “To amma saboda Allah me yasa ka kirani adaidai lokacin da …