ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER  4 by Sumayyah Abdul-kadir  Www.bankinhausanovels.com.ng  gadi, na kuma ga gilmawar taurari goma. Amma bakina bai mutu ba.  “Muddin ka iso gareni sai dai wani ba kai ba, baka ba da saki amma idan ka tafi inda Nazir ya tafi na saku ko babu takaba, iyakaci nima a kasheni. Na gwammace mutuwar da zama da kai wai a matsayin miji sau dubu gara mujiya da kai Fa’izu Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa”.  Wani irin karfi da ban zata ba ya shigeni, na isa ga madubin dogon yaro dake like jikin bango wanda Abdallah yasa kusoshi shida ya kafa a dakinsa na soma kokarin banbaro shi daga jikin bangon, ban damu da yankewar da tsokar hannuna ke yi da gilashin ba har na samu_ nayi nasarar raba shi da kusoshin da suka tokare shi suka zame masa garkuwa daga fadowa kasa. Fa’izu Abubakar, ya tabbatar tsandara mishi mudubin nan zanyi, wanda hakan na_nufin tsattsagewar jikinshi ta ko ina, alhalin ba karfinsa nafi ba, don haka yayi amfani da wani irin zafin nama wurin isowa gareni, ya kama m…