ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir  Www.bankinhausanovels.com.ng  samu sauki daga azabtuwar da zuciyarshi ke yi a dalilin rashin ganin nata, inyaso ko ganinta ya yi kawai daga nesa ya haura takalmansa ya bar mata garin da kasar baki daya, in ta rage bala’in ta bishi Amsterdam su zauna. Indai sun kasance gida daya ai maganar kafiya da kiyayya sai ayi ta yin mai dalili, ba yanzu da ko harararta baya hange ba.  Ya kurawa jerin jakunkunan da ya danqara dalolin shi ya sayo da sunan lefe ido. Shin wacce Fa’izah yake tunanin za ta daura zaninshi? Ko da yake a lokacin yana kan aiki a Istanbul ne, giyar son ta buge shi, ya shiga hada su a kasuwar (AKMERKEZ Shopping Mall) ba tare da ya yi shawara da kowa ba ko yasan ‘size’ da take amfani da shi a yanzu. Ya dubi shekaru ne kawai ya kintata, kuma da ya ganta bata zarce yadda ya kintatan ba.  Ya bude yana duba su a hankali har da (underclothes). Fadin abinda ya kashe akai bata baki ne, amma ta wace hanya zai bata ta karba tunda a …