ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir kai da suka ci kwalliya kyawu na bugun kyawu, duk hawaye ya vata kyakkyawar fuskar Bamallin su. Muftahu kam girgiza kai yake. Ali Na’’ibi, ya jingina da bango, yayin da maganganun da suka yi da Fa’iza ke nausar kunnensa tamkar a lokacin ne take yi. “…ko yankani za kuyi A.B bani auren nan… na gwammace in bi YAWON DANDI… da dai in qarashe rayuwata a matsayin matar FA’EEZ BAMALLI!!!”. Aliyu ya kama kai, ya ce, “Kash! Kinyi kuskure babba Fa’izah, ko masu yawon dandin basu da aure akansu, kada kiyi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba mana…”. Ya fisgi hannun Miftahu suka yi waje inda ya xauki motarshi aguje suka bar garin Giwa. Allah Sarki Aliyu xan uwa na gaskiya, gidan karuwai ya riqa bi kala-kala da Miftahu wai yana neman Fa’izah, yana mai suffanta musu ita tare da nuna hoton ta. Amma babu wanda ya ce ya ga gilmawar ko mai kama da Fa’izah, amma babu alamar gazawa a tare da shi. Miftahu kam ko fitowa daga mota bai yi ba, tausayin Aliy…