ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER  12 KARSHE THEND by Sumayyah Abdul-kadir                  Www.bankinhausanovels.com.ng  nake jira. Na zauna na ci son raina na koshi, har da kara tea bayan na shanye kofi guda. Naji ni dai-dai, nayi hamdala ga Allah. Na kwance daurin da nayi na dankwalin atamfata na yafa da yake dankwalin babba ne sai ya rufeni ruf. Na nufi kofa na tsaya. Ya mike ya fito falon ya jingina da kofar da ta raba uwar dakin da falon, ya ce. “Au, baki ji abinda na ce ba ko? Tunda kunya kike ji dauki biro da takarda ki rubuta min kinji sabuwar kurma?” Ban musa ba, sai dai a raina na ce, “Inji kunyar ka? Amma da nayi asara. Kunyar maras kunya al asara ce!”. Na dawo na dau takarda da biro na jingina da bango na soma rubutu. Da na kammala na aje nan, na sake komawa bakin kofa na lafe. Ya dauki takardar ba tare da ya bude ba ya sanya a aljihu ya taho yana fadin. “Kin manta da guzurinki”. (Yana nufin sanitary pard). Ban bashi amsa ba ya shiga (toilet) din ya kullo duka kayan a ledar da ya…