ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir Www.bankinhausanovels.com.ng neman dacewa duniya da lahira”. Da ace Fa’iz yasan tashin hankali da bala‘in da kalaman dake fita daga bakinsa suke kara jefani da ko da wuka a makoshi bai yi gigin furta su ba. Domin kalamai ne da ban taba jin mafi muninsu a duniya ta ba. (Hada rayuwa ta har abada da shi FA’1Z-ABUBAKAR) koko ince makiyina. Mugun dan uwa da kullum ketowar alfijir da faduwar rana sai nayi dakacen INAMA ban hada jini da shi ba. Wani kwayan mutum guda daya da ya maida mahaifiyata marainiyar wayonsa, ya maida ni kwallon takawarsa a duk sanda ya so, ko gare-gare abin wasan yara. Mikewa nayi gaba daya na littafin KWANA SITTIN ya fado daga ruwan cikina, na ce. “Da uwar wa Zaka tafi wurin direbancin?” Tsalle daya nayi sai gani a bakin kofar dakin nayi maza na rufe na murza ‘key’ na zare shi na cilla shi waje ta taga cikin wani irin zafin nama da ni kaina ban san inada shi ba. Ya yi maza shima ya cafe mukullin…