ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN  BOOK 3  CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir  Www.bankinhausanovels.com.ng  Mai taxin ya gaji da gaya min gamu cikin Zaria, ina zamu dosa? Na zama kamar mutum-mutuma, kurma, makauniya don tunani, saida ya bubbuga kujerar danake zaune nace masa gida mai lamba tamanin cikin gidajen malamai na jami’ar Ahmadu Bello. Gidan da ya zamto mahaifata, dandalin quruciyar rarrafe da tata-ta ta, kafin in gu jeshi zuwa inda nake ganin ya fishi farin ciki da walwala, a yau gani na dawo da qafafuna, na kuma gwammace in qarashe sauran rayuwata cikinsa ko da ace yafi kurkuku rashin daxi da taqaita farin ciki.  Wata irin doguwar ajiyar zuciya na saki, na ciro kuxin da suka rage min kaf ko girgawa banyi ba na baiwa mai tasi, ya fitar min da jakata daga bayan motar sa, ya yi min godiya mai yawa ya ja motarsa ya bar harabar wajen.  Zan iya kimanta lokacin da garfe takwas na dare sanda nake tsaye qofar gidanmu, domin ina iya hangen tangareren agogon falonmu wanda hasken qwan lantarki ya wadata, kuma an …