ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir ran Fa’izah ba. Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba….. Surutun Hajiya kara kular da shi yake. A kufule ya ce, “To na ji Hajjah, in ta farfado din sannan ki san abin yi ko ba yanzu ba da lafiyarta ake nema ba komai ba”. Hajjah ta wuce tana fadace-fadacen ta da mita wanda Fa’izu bai saurari ko daya daga cikinsu ba. Pilot Fa’iz Giwa babu abin da ya gama shi da asibiti. Amma tsabar kishin kada Aliyu ya daukar mishi mata ya gwammace kada a kaita asibitin. Shi kam yanzu ya fara son Fa’izah ma da damarar rayuwa da ita. Sai dai ta mutu su je lahira suyi aure su zauna tare, amma Hajjah ta canza masa farat daya kamar ba Hajjar shi ba wadda ta fi kowa son shi a duniya including iyayenshi, ta fi shi son duk abinda yake so, ta fi kowa farin ciki da ya ce a aura mishi Fa’izah ba. Ta yi murna, ta sa mishi albarka har da kukan farin cikinta. Amma da ya dubi halin rai kwakwai mutu kwakwai da Fa’izar ke ciki sai ya yi mata…