ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir Idona ya cicciko da kwalla kadan ya rage su shimfido a kundukukina, na ce, “Yaya Aliyu ka taimake ni ina son Naziru, ina tsoron halin da zan shiga in na rasa shi. Fadar A.B ba fadar Allah ba! Bani da wanda zai taimaka min ya shige min gaba idan ba kai ba. I cannot afford losing him…” Yaya Aliyu ya zuba min ido na san mamakin halinmu na mata yake yi, a raina na ce, “Har an fika Aliyu Haydar?’ Ya saukar da kai bisa yatsun Fa’izah karama dake bisa cinyarsa, ya ce, “To ni dai Fa’izah babu abin da zan iya a kan wannan rigima da kika je kika jajibo. Zan yi dai iya kokarina in ga cewa ba a yiwa dangin Nazir wulakancin da za su tafi damu a baki ba idan sun zo. That is all. Ki jira hukuncin Hajjah a gobe”. Tun daga nan jikina ya kara yin la’asar. Na tashi na bar Yaya Aliyu don a ganina ba shi da abin da zai iya yi min din da gaske kamar yadda ya ce. Karfe tara na dare na kira Maman Kaduna nake sanar da ita zuwan dangin Nazir a gobe, don …