ZAFIN SO COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAFIN SO COMPLETE HAUSA NOVEL
ZAFIN SO COMPLETE HAUSA NOVEL                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Tafiya muke nida Hanee ko waige bama yi, da abn yayI nisa ma har gudu muka koma yi duk dan muga mun tarar da wannan hamshaqiyar yarinyar, bamu muka tsaya ba sai bakun wani qayataccen gida wanda da ka ganshi gasan na wani mai muqami ne, a daidai vakin gate yarinyar ta tsaya da motarta qirar range rover ash colour, horn tayi amma shiru ba’a bud’e gate ba, sai bayan kamar minti biyu ta qara wani horn d’in amma shiru gate man bai bud’e gate d’in ba. A fusace ta fito daga mota ko jakarta bata d’auka ba ta bar motar bud’e ta shiga gidan. Koda shigarta ta samu gate man d’in kwance yana rawar sanyi alamar baida lafiya, bata ko duba yanayinshi ba ta d’aga hannunta ta wanke shi da mari, dafe kumatunshi yayi wani zazzafan hawaye na saukar mishi, kafin ya ankara ta qara d’auke shi da wani marin, sai a lokacin tace “kai uban waye da zanyi maka horn har sau biyu amma ka kasa bud’e min gate? Bayan kuma kasan bisa ga d’abi’ata…