YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Idrisu ya amsa masa da cewa, “Baba wannan kada ka damu kanka, don in Allah Ya so matuKar dokina Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora yana tare da ni, to ba na tsoron nisan tafiya ko kuma wahalarta, kuma ma ina tabbatar maka da cewa in Allah Ya so tare da Sarkinku za mu yaki azzalumi Sham’una.” Aka shirya gagarumar walima, aka ci aka sha, suka yi ta murna da raye-raye irin nasu na aljanu. Babu shakka Idrisu ya ji dadin wannan karramawa da aka yi masa. Aka nuna masa dakin da zai sauka, saboda girman dakin gaba daya shi da Jagora suka shige, ko da yake zuwa yanzu ya fara daina mamaki game da irin aikin aljanu. A haka, kuma cikin matukar jin dadi da farin ciki sai da ya kwana bakwai yana hutawa, jikinsa ya warware. Daga nan sai ya sanar da Shehi Abdallah Limamin aljanu cewa shi fa yanzu ya yi harama yana bukatar wucewa, kuma ya gode game da dukkan irin tarba da kyautatawa da ak…