YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  16 BY HARUNA USMAN                 Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?” Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.” Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan’uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.” Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk ‘yan’uwa muke ba mu sani ba?” “Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su. Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.” A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sam…