YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA  Sham’‘una ya tambaya, “Su wane ne shugabannin yakin.” Wani aljani da sarautarsa ke matsayin Magayakin birni na sha dayan ne ya amsa masa cewa, “Wuta da rana su kare ka, wani jarumi ne dan Adam ke shugabantarsu, yana kuma yi mana muguwar Barna, ya kashe:-mana dakaru da jarumai babu iyaka, yana kakkarya wuyaye kamar da sihiri, wannan babu shakka karawa da shi sai kai. Kuma ran sarkin aljanu ya dade, a can gefen Gabas Sarki Ifritu ne rike da wani gwalmi, duk bugawa daya , aljanu kusan ashirin ke zubewa. Daga gefen Arewa akwai wani jarumi da suka zo da shi wanda babu ko alamar cewa ya yi niyyar barinmu da rai, don kuwa yanka ya ke yi kamar yana wasa.” Zuciyar Sarki Sham’‘una ta yi kunci, fuskarsa ta sauya, gashin girarsa ya mike tsaitsaye, idanunsa suka yi jawur kamar garwashin wuta, bakinsa kuma sai wani irin tururi ke ta fita don tsananin fushi. – Sharri da’ sake-sake suka cika z…