YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 6 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 6 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 6 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Lokacin da suka zama su biyu sai Idrisu ya gutsura wa Sarki wani bangare daga cikin labarinsa, ya ce, “Ya kai wannan Sarki ni matafiyi ne, ina so zan je wurin wasu tsibirai ne can a bayan duniya. Dalili kuwa shi ne don in yaki wani mugun aljani wanda ya sace ‘yan mata ‘ya’yan mutane ya tara su a can, su kamar hamsin da doriya. A can ya yi musu gida, kuma su wadannan duwatsu suna cikin wata babbar teku ce. Wannan wuri yana da wahalar zuwa.” Da Sarki ya ji zancen Idrisu sai ya yi wuf ya rungume shi yana zub da hawaye. Ya ce, “Ya kai Idrisu ina maka fatan nasara. Ka gan mu nan mu ma mun fito neman ‘yata ne. Ita ke nan guda daya a wurina, na karantar da ita fanni daban-daban na ilmi, ina alfahari da ita, ina sonta so mai yawa saboda hankalinta. Muna cikin shirye-shiryen yi mata aure da wani saurayi wanda shi ma bako ne, sai abin da ya ZAMU TASHI faru ya faru Shi wannan saurayi yanzu …