YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  27 KARSHE END BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Dailanu tana fita sai ta yi wa jama’arta nuni, ai nan da nan suka sungumi gida, tana gaba suna biye har tsakiyar dumbin aljanun nan da ke fagen fama sannan aka sauke shi. Aljana Dailanu ta shiga ciki, Www.bankinhausanovels.com.ng  can bayan wani dan lokaci sai ga ‘yan matan nan gaba daya suna biye da ita. Wannan al’amari ya yi matukar bai wa jama’ar aljanu mamaki, suka Kara tantance cewa wato a banza ke nan Sham’una ke daukarsu tun da har ba zai iya soyayya da ‘ya’yansu mata ba sai dai na mutane. Ai nan fa suka yi ta tsine masa, kuma zaluncinsa ya Kara bayyana a gare su. Wasu daga cikin jama’ar da ke wurin sai suka yi ta cewa, “A fito mana da azzalumi, a fito mana da mugu.” Aka kuwa fito da shi daga cikin battar Karfe, daure cikin sarka. Wasu daga cikin ‘yan matan nan suna kuka haka suka rika tashi suna bayyana irin yadda Sham’una ya rabo su da gidajensu da masoyansu ya mayar da …