YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  10 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA  Sarki ya fuskanci malam ya ce, “Malam Ahmadu ka ga wannan lamari mai bakanta rai dai? Ni kuwa in har Www.bankinhausanovels.com.ng  wannan magana ta tabbata gaskiya, to zan zamo wanda ya fi kowa mamakin mata, don irin yadda na amincewa wannan mata, na sakar mata komai, na kori sauran matana saboda son da nake yi mata. Kuma Allah gafarta malam, saboda amincewar da na yi mata, ta sa na wulakanta ‘yata har na sauya mata gida. Don ma a wancan lokacin na yi dacen daukar shawarar wasu mutanen kirki cewa kada in sa a sare wa ‘yar tawa kai. Malam in har wannan magana ta tabbata, to daga yanzu matan Kasata kaf za su riKa wahala kamar yadda mazaje suke yi, har yaki za su rika zuwa, kuma za mu sa su a gaba sai an fara kashe su tukuna kafin maza su shiga, kai har da ‘yata duk za a hada, don ba zan kara saurarawa wata ‘ya mace ba.” Sai malamin ya ce, “Allah Ya huci zuciyarka, ai laifin wani b…