YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 25 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 25 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  25 BY HARUNA USMAN                      Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Yanzu al’amari fa ya sake Kazancewa, Sarkin aljanu Sham’una a nasa bangaren sai murmushe aljanu ya ke yi kamar yana murmusar soyayyar gyada, babu ko Shakka ya isa Kasaitaccen jarumi, saboda sadaukantakarsa duk inda ya fuskanta sai a dare a ba shi wuri. Shi ne da kansa ya ke bi da gudu yana kamowa yana kashewa, amma ba dai a tarbe shi ba. A’a, Sarkin aljanu Sham’una ya wuce haka a wurin gama-garin aljanu. Www.bankinhausanovels.com.ng Ran nan sai Karajin mazaje kake ji da hargowa, da ma ko fadan mutane ne yaya, ballantana kuma na aljanu har ma da manyan jaruman sarakuna irin Sham’una da Ifritu? A takaice dai kwanaki ashirin da daya da aka yi ana ta gwabzawa kafin a rabu don hutawa da kuma sake shiri, kumaa cikin kwanakin nan daidai da rana daya Bangaren Sarkin aljanu Sham’una bai taba samun nasara baa kan daya bangaren. Tsananin yawansu ne kawai ya sa ba a saurin gane i…