YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 22 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 22 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  22 BY HARUNA USMAN                    Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Tafiyar wannan gagarumar runduna ta su Sarkin Www.bankinhausanovels.com.ng  aljanu Ifritu da jarumi Idrisu a sararin samaniya, da a ce mutum zai ji rurinsu, to babu shakka zai hakikance cewa duniya ce za ta tashi. Wannan runduna ba ta bata wani lokaci ko kuma wani hutawa ba saukarsu gari na farko sai suka yi fata-fata da shi. A irin wannan karon ma ko damuwa da kama aljanu ba su yi ba, kisa kawai suka yi ta aiwatarwa, kuma ba su kyale duk wani kakkarfan aljani ba. “Yan kadan da suka tsira suka ruga zuwa gari na biyu suka sanar da su irin bala’in da ke tafe. Aljanun gari na biyu suka shirya cikin gaggawa suka fito don tunkarar abokan gaba. Kwana biyu kawai ana gwabzawa aka ragargaji wannan gari, masu tserewa suka tsere. Abin da kawai wannan runduna ta Idrisu da Sarki Ifritu ba sa tabawa shi ne basa kashe Kananan yara da tsofaffin aljanu, wato sabanin Sarki Sham’una wanda i…