YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Da suka ga haka, sai suka fara rikidewa suna komawa wasu irin macizai, iri-iri, launi dabandaban, jajaye da farare, algashi da masu dabbaredabbare, kai wasu ma har da dan kunne. Wasu manya kamar girman giwaye, wasu kuma Kanana. Wasu na kukan jaki wasu suna haniniyar doki, kai wasu har tashi sama suke yi suna sauka. Lura da haka sai Idrisu ya zaro takobinsa daga kubensa, kuma wani abin mamaki shi ne takobin na fitowa sai kawai bakunansa suka koma goma sha biyu, kuma dogaye masu tsawon gaske. Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka fara kai masa hari, amma da zarar ya kai sara sai ka ga aljanun macizan nan suna ta fadowa kasa kamar fari, kafin wani dan lokaci ya kashe duk macizan da ke shawagi a kansa da kuma wani kaso mai yawa daga cikin wadanda ke Kasa. Sauran sai suka raba junansu kashi-kashi, koraye daban, jajaye daban, tika-tiKka daban, haka nan sirara, ga su…