YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  14 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA Sarki ya ce, “Ku dai samarin wannan zamani al’amarinku sai ku, yanzu kowannenku ya bar yankinsu, ya shiga cikin hadarin neman yarinya? Kun san halin mata kuwa? Ko da yake yanzu dai duk a Kyale wannan zance. Shin ka yi nasara game da abin da ka fita nema?” Yarima Amir ya ce, “A’a, Allah Ya taimaki Sarki, amma na sami labarin inda za mu iya samun labarinta. Shi ne na dawo in shirya in sake fita, an ce can kasar Arewa akwai wani Sarki wanda shi ma hakan ta faru ga ‘yarsa kuma an tabbatar cewa yana da cikakken labari. Daga wurinsa kuma sai in tsunduma duniya neman ta.” Da Sarki ya ji zancen dansa sai ya ce, “Ya kai dana, ina ji maka tsoron yawo cikin duniya, ka dai ga dan Karamin misalin abin da ya faru ga abokinka, mafi yawancin jama’‘arsa sun rasa rayukansu, kuma ga shi kai ne mutane suka sa wa ido a matsayin magajina. ZAMU TASHI Sai dai kuma soyayya ta rufe maka idanu ko mulkin ma naga kam…