YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 8 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 8 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 8 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Ni ne Sarkin lambu, akwai masu aiki nan kamar mutum dari Karkashina, yau ranar hutunsu ce, kuma a irin wannan ranar ne Sarki kan zo gewaye, shi ya sa ba ka ga kowa ba.” Sarkin lambu ya ci gaba da cewa, “Babu shakka ina da tambayar da zan amsa a kan wannan gwanda da ka tsinko. In Sarki ya ji, in ban yi sa’a ba yana iya yanke mini mummunar hukunci don a gaskiya Sarkin namu yana da zafi. Abin da kake ganin ba a bakin komai ya ke ba, shi wannan Sarki sai ya dauke shi da babban muhimmanci don ya sami damar hukunta mutum.” Da Yahaya ya ji jawabin Haladu Sarkin lambu sai yace, “To tun da yake haka ne, mu gudu mana kafin Sarki ya iso.” . Mai lambu ya ce, “Yaro dai yaro ne “in na gudu to lallai Sarki zai yi zaton akan wannan gwandar daya ne, saboda haka zai ‘sai a kama iyalina yasa a kashe su ZAMU TASHI Ka ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ke nan. Ina ranar da namiji zai gudu ya bar…