YAKANA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA  BOOK 2   CHAPTER 6  BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  hakan bai sa tunanin yarinyar ya barshi ya huta ko na second daya ba, kamar yadda ya yi tsammanin nisa da ita shi ne hanya mafi sauki da zai yaki soyayyarta.  Ashe hakan tamkar zubawa wuta kananzir ne, tunanin sa na cewa yin nisa da Fati shi ne babban makamin yakin soyayyar ta a zuciyar sa ashe ba shi ne maslaha ba.  Ta riga ta yiwa zuciyar shi kamun kazar kuku, ta yadda dai-dai da rana daya tun tahowar sa zuciyar  sa ba ta tava hutawa ko na dakika da tunanin ta ba.  Dr. Smith ya iske shi a hakan, ya dade yana magana bai san yana yi ba. Kafin dan lokaci ciwon ciki ya turnike shi, ya kama cikin ya soma juyi, sai ya fado bisa kilishin dake shimfide a farfajiyar wajen.  Da sauri Dr. Smith baturen Chicago ya kama shi ya soma binciken abin da ke damun shi, tare da ba shi taimakon gaggawar duk da ya dace.  Bai samu kansa ba sai bayan awanni biyu, lokacin ciwon cikin ya lafa. Ya sa ido yana kallon Dr. Smith wanda ke shan …