YAKANA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 5 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA  BOOK 2   CHAPTER 5  BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika. Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa. Kallon ta yake yana (observing) da ido, da zuciya. Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha’awa mai yawa.  Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi. Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kadawa. Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba.  Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu ‘yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online.  Ta dan ware ido tana kallon sa da a…