YAKANA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA  BOOK 2   CHAPTER 4  BY SUMAYYAH ABDULKADIR Www.bankinhausanovels.com.ng  hammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr. Hadizah…… ‘“‘Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Allti. Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin’”’.  Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”.  Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama.  Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba.  Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsana…