YAKANA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA  BOOK 2   CHAPTER 2  BY SUMAYYAH ABDULKADIR wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko kazama da mai tsafta.  Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an kuma sha baki kyauta a kanta. Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba.  Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a’a, Fati kina da shi, HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namiiji……… Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta, “Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?”  Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, “A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma a zaman aure bai fi karfin ki ba. Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba. A‘’a, maintain your own kualities (rike taki sigar).  Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali, ilimi da…