WA NAKE SO CHAPTER 27
WA NAKE SO CHAPTER 27 Www.bankinhausanovels.com.ng Fulani ki shiru kawai!” “Bazan ba Ranka ya Dade kayi ba dai dai ba Kuma dole nai magana.”+ “To kiyi!” “Ai nayi Dan haka baka kyauta ba ka dawo da ita.” Kan gadon ya hau yace “Bacci nake ji Fulani kinzo Zaki hanani Bacci taho mu kwanta.” Ya fada Yana kamo hannun ta. Kwacewa tayi ta mike tsaye ta karasa bakin kofa tace “Ban yadda ba Kuma Ina kan baka na ka dawo da matar ka shikenan Kuma ba a laifi Dan tayi kuskure mu Allah ne ya dauke Mana da bamuyi ba. Kana zaune Allah zai iya jarabtar ka shin a lokacin me zaka so? So zakai a yafe maka! Dan Allah ba Dan ni ba ka sassauta mata.” Ta fada tana hade hannayen ta biyu. “Ban San saki nawa kayi ba Amman ina fatan bai haura daya ba. Sai da safe!” Ta fada ta juya ta fita a dakin. Kallon Kofar yabi da kallo ya girgiza Kai yana fadin “Ko Zan dawo da ita ba yanzu ba.” Ya koma ya kwanta Yana Jin son Mamah a ransa Dan yadda take saka sa a hanya in ya kauce. Addu’a yayi bacci ya dauke shi. Tin asub…