WA NAKE SO CHAPTER 21

WA NAKE SO CHAPTER 21
WA NAKE SO CHAPTER 21 Yana shiga daki ya zauna yana dafe kan sa. sai kuma ya mike ya cire kayan jikin sa wanka yayi ya fito ya saka kayan bacci. Wayar sa ya dauka ya fara neman layin ta. Tana cikin shirin bacci taji wayar na kara karasawa tayi ta dauka tayi sallama bayan ya amsa tace ‘Ya gajiyar hanya?”+ “Alhamdulillah i miss you ne kawai ina son na jiki a jiki na.” “Hmmm!” “Wallahi My Hearrbeat ban san nayi kewar ki ba sai yanzu da nake son na ganki gani gaki na dan ji ki a jiki na.” “Hmm ina Yaa Muhammad?” “Yana gida ai nima ban jima da dawowa ba naje naga Yayen ki su umar,  İbrahim,  Mustapha da Shu’aibu suna da hankali abun da ya fi min dadi ma yadda su Umma suka tarbe ni naci tuwon Umma mai dadi saura kadan kunne na ya cire dan dadi.” Dariya tayi tace “Tab da ya cire ban zama dame kunne daya.” Yai dariya yace “Ko?” “Eh mana!” “Allah Baby love abincin yai dadi zakina min irin sa.” Tai murmushi tace ‘İnsha Allahu.” “Thank you. Ya na baro ki kina kewa ta?” “Sosai ma. Duk ba dadi kamar ban d…