WA NAKE SO CHAPTER 20
WA NAKE SO CHAPTER 20 Www.bankinhausanovels.com.ng Su Mamah na sauka aka aiko aka dauke su. Lokacin da suka shiga gidan Aisha ba karamin mamaki tayi ba domin bata zata nan ne gidan ba bata san waye Abbah ba sai da taga yadda ake musu abu ne tace “Wai ku daman jinin sarauta ne?” Murmushi Maryama kawai tayi suka shige shasjen su ana tai musu barka da zuwa. Dakin su Maryama suka shige. Ruwan wanka Maryama ta hada mata ta shiga tayi wanka ta fito Maryama tayi. Sallah tayi tana idar wa Maryama ma ta idar. Suna zaune daya daga cikin masu musu hidima ta shigo da kayan abincin su. Zama sukai suka ci suka koshi sannan suka bare suna hira. Maryama tace “Wai baki san waye Yaa AK ba?” “Eh! Please fada min!” “Ba ruwa na kyaji daga bakin sa. Amman dai Abbah shine sarkin garin nan.” “Sarki fa kika ce!” Kai ta gyada Aisha tace “Ikon Allah Amman Abbah ba ruwan sa ba wanda zai ce haka saboda bashi da wani izza da daukar kai.” Dariya Maryama tayi. Aisha tace “Wallahi kinga fa yadda muke rayuwa dasu daman haka sara…