WA NAKE SO CHAPTER 18
WA NAKE SO CHAPTER 18 Www.bankinhausanovels.com.ng Zaune suke Najah da Khady sai Jidda. Jidda ta zuba tagumi tana kallon su. Najah ce ta ce “Ji yadda kika koma akan kishiya kawai na fada miki ki kwantar da hankalin ki amman kinki ko?”+ “Hmm tayaya hankalina zai kwnata daga cewa jibi zakizo yau sati nawa Najah kenan damuwa ta ba taki bace ko?” “It is not that Jidda ki tsaya kiji me ya zaunar dani.” “Ina ji.” “Na raka matar Sarki china ne.” Tsaki ta saki tace “Dan ta fini arziki kenan ko?” “Dan wa naje in ba dan ke ba Jidda wallahi danke na bita.” “Ni kuma?” “Eh mana wajen wani malami na rakata nima anan na bada bukatar ki kuma yace in jira kawai amman fa da matsala.” “Tame?” “Yace kan bikin dole na koma kamar da sati biyu haka!” “To ya za ayi Najah ina naga kudin da zan baki kije china.” “Hmm kada ki damu zamu koma da ita to kinga dalilin da yasa kika jini shiru fa.” “Amman nagode na zata kin manta dani ne.” “Wallahi kina raina.” “Thank you.” “Yanzu saura wata nawa?” “Wane din wata nawa? Wata nawa aka sa…