WA NAKE SO CHAPTER 16

WA NAKE SO CHAPTER 16
WA NAKE SO CHAPTER 16 Www.bankinhausanovels.com.ng  Yana shiga daki ya zauna a bakin katifar sa yana mai rike kan sa. Tausayin Aisha na kara ratsa zuciya da dukkan jikin sa. Hakika bai taba kawo wannan ranar a ran sa ba wacce zai iya cire son Aisha a ransa amman dole ya daure yayi haka ko  dan yin biyayya ga Umma sannan ko dan samuwar farin cikin Aisha.+ Yana son Aisha har bai son adadi ba lallai zai mata abinda take so ko ta samu sauki a ranta. Yana zaune Umma ta shigo rike da kwanon abincin sa. dagowa yayi ya kalle ta. ta ajiye tace “Ban fada maka wannan maganar dan kaima ka sa damuwa a ranka ba,  na fada maka wannan maganar dana warware wannan matsalar ina fatan ka gane.” Kai ya gyada yace “Insha Allahu komai zai warware Ummah na.” “Allah maka albarka ka ci abincin sai da safe!” Ta juya ta fita. abincin ya dauka zai ci sai yaji ina ba zai iya ba taya zai iya cin abinci zai rabu da masoyiyar sa. Dukka tsarin sa da komai akan Aisha yayi su yanzun komai zai tarwatse masa kenan. Alwala yayo ya…