WA NAKE SO CHAPTER 12
WA NAKE SO CHAPTER 12 Aisha ce zaune ta yi zugum tana tunanin rayuwa, ba wanda take tsananin so da bukatar gani sai Yaa AK. Tin jiya da ta bacewa Yaa Muhammad bai kara ganin ta ba. Dan daki ta shige tana jin sa kuma ta kwanta kamar mai bacci wannan yasa bai tashe ta ba.+ Tana son kasancewa da kowa a cikin su ta kasa gane wanda tafi son kasancewa da. Tasan tana son Yaa Muhammad amman meyasa zuciyar ta take kawo mata tunanin Yaa AK wanda har bata da abun yi sai shi kuma shi ke debe mata kewa. Yaa Muhammad ne ya shigo dakin ta, tana ganinsa ta yi saurin bude littafi kamar mai karatu. Zama yayi a gaban ta ya ce, ‘ “Aisha tawa ana ta karatun ne?” Murmushi kawai tayi tai kasa da kanta. Dan satar kallon sa tayi taga ya zura mata ido hakan ya sa ta yi saurin kau da kai. Yana kallon ta yace “Ya karatun to ba wata matsala ko?” “Yaa A…..” Sai tai shiru kuma. Kallon ta yayi yace, “Mutumin nan yana da matsayi mai yawa a gun ki Aisha, wanda har kina mantawa kina kiran sunan sa, ko duk dan ya tafin ne ko…