RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.” Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.” Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa …