RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Nasreen ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ya sunkuya dai-dai fuskanta yana gaya mata kalamai a hankali kuma ya dinga hura mata iska a fuska, tana jin kasala tana shigarta, hade da barci wanda ba ta san lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba. A fili yace, “Allah ya baki lafiya Wife.” Ya sumbaci goshinta ya fice. A falo ya sami Umma da hafsat fuskar nan tata ta kumbura gwanin ban tausayi. Www.bankinhausanovels.com.ng Har zai wuce Umma ta ce, “Zo nan ina son magana da kai.” Babu musu ya dawo ya zauna yana duban Umman, sannan ta fara magana, “Ka ji tsoron Allah Sultan ka gaya min me Hafsat ta yi maka haka da zafi da har kayi mata irin wannan dukan? Gaya min me ta yi maka? Idan babu laifin da ta yi tsabar mugunta ce kawai, ka gaya min sai in dauki mataki.” Sultan bai ji dadinl da Umma za ta yi masa magana irin hakan a gaban su Hafsat ba, wannan kamar ta ce gobe…