RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA  BOOK 3   CHAPTER 6 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO                       Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Sultan ya rage kayan jikinsa ya zauna kusa da ita tare da cire mata Hijabin, gashinta da yake ta walKiya suka zubo kafadunta. Ya _ tura hannunsa yana yi mata susa, “Nasreen ina shan wahalar rashinki a kusa da ni, Umma kuma ta kafe ta tsare. Bansan ya suke son in yi da rayuwata bane. Yanzu kin ga Hotel muka zo zan samu in yi barcin da na rasa zuwa anjima sai mu je mu dauke su. Karki damu idan suka sha wahala gobe ba za su sake cewa za su biyo mu ba. Ita Zakiyyan duk irin dadewar da muka yi tare, ai ya kamata ta daga min Kafa tunda babu laifi na sauke dukkan hak KoKinta.” Nan take fuskar Nasreen ta sauya, da gaske take jin kishinsa akan Zakiyya, ta fi son abinda bata sani ba, akan alaKarsu ta boye sirrin su, idan ya bari tana jin irin wannan kalaman za ta iya shiga wani hali na kishin da halitta ce a jikin mace, sai dai kowa da irin yanayin danne kishinsa. Sultan ya K…