RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA A hankali ta yi magana, wanda da ba don yadda ya tattaro natsuwarsa akanta ba, da babu abinda zai ji, “Na amince Deena, duk abinda ka yi dai-dai ne, ina jin tsoron Umma ne shi ya sa, kuma ta ce min in daina zama a falo. Ban san me na yi wa Umma ba bata sona Dee, ban san me zan yi wa Umma in burge ta ba, ban san mene ne musababbabin wannan tsanar ba, don Allah ka sanar min dalilin ka gaya min idan laifi na yi mata zan ba ta hakuri.” Ta fara fitar da hawaye, ya sa hannunsa ya dauke hawayen yana sake duban ta, “Ba ki yi wa Umma komai ba, ban san mene ne dalilin da ya sa Umma take gwada maki irin wannan tsanar ba, kamar ba jininta ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng Nasreen ta girgiza kanta, “Ka daina zolaya ta da irin wadannan maganganun Deee, tuni na yi hankalin bambance fari da baki, na sani, da ni da Nawfal ba jininku ba ne, ba mu da wata alaka da ku, na sani akwai wan…