RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA  BOOK 3   CHAPTER  3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO                       Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Jiki a sanyaye ta mike har ta kai bakin ‘kofa ya ji a zuciyarsa bai kyauta ba, da ya yi mata hakan, ya tabbata da Nasreen ce ta shigo cikin bargo zai maidata. Ya zama dole ya jinga Kokari wajen ganin ya bi shawarar nahaifinsa. “Zakiyya.” Ya kira sunanta cikin sanyi. Ta waiwayo cike da mamaki. Har hawaye sun sami daman zubowa. Gabansa ya fadi, domin ya san kai tsaye gun Umma za ta wuce. Hannu ya mika mata, hakan ya sa ta dawo da sauri ta kama hannunsa ya zagayo da ita kusa da shi. Hijabin da tasa ya yaye sannan ya hadata da jikinsa. Warin attachment din kanta da Karni suka dake shi, ya dan kawar da hancinsa sannan ya fara magana cikin lallabawa, “Zakiyya ba na son ina bata maki rai amma ke kike sawa. Ki yi hakuri kin ji? Ba na son a yi maki kallon mara kunya ce, ki koma cikin jama’a.”Www.bankinhausanovels.com.ng  Zuciyar Zakiyya fari sol! Ji take yi kamar duk duniya ba…