RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sultan ya sake jifan bangon dakinsa da murmushi, ba tare da ya lalubo abinda zai gaya mata ba. Tsintar muryarta ya yi tana cewa, “Na so in riga Nawfal fara ganin fuskarka, naso inga irin kyan da na ji ana kururutawa ka Kara, sai dai hakan bai yuwu ba sakamakon makanta da ta toshe min idanun yin hakan. Sai dai kafin Allah ya karbi idanun da ya bani aro, ni shaida ce Dee mai kyau ne, Dee yana da kwarjini a idanun kowa.” Kalaman yarinyar suna yi masa kama da mai son cusa masa rauni a Zuciya. ““Nasreen kada ki damu za ki gan ni da zarar muka ci karo da Dokto din da zai yi maki aiki.” Www.bankinhausanovels.com.ng Cikin rauni ta ce, “Don Allah zan roKe ka wani abu. Amma sai a ranar da Za a yi min aikin.” “Allah ya kaimu ranar.” Ya mayar mata da amsa yana jin barci yana son kwasarsa. Zakiyya ta shigo dakin tana Kare masa kallo, “Da waye kake waya?” Firgigit ya bude ida…