RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 10 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA sandan ya ce, “Sorry sir! Mun so mu hana su, madam ta fito ta zage mu ta ce su shigo.” Sultan ya daka masa tsawa, “Ka yi min shiru bana son bayanin nan. Ita kuke yiwa aiki a gidan nan ko kuwa ni? Daga yau babu wata mace da za ta sake sa doka wani a cikin ku ya bi, ba tare da ya tuntubeni ba. Saboda kune sakarkaru har ayi wannan abun tsawon kwanaki babu wanda ya taba gaya min? A kan me?” Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, za su iya rantsewa tunda suka fara aiki da shi, ko tsawa babu wanda ya taba yiwa, amma yanzu harda mari, lallai ankai shi Karshe kenan. A fusace ya taka ya shige dakin Zakiyya. Tana zaune tana waya tana bada labarin yadda suka kasance da Sultan, wanda karaf a kunnensa. A duniya ya tsani mace mara sirri, ji yake kamar ya shaketa ya huta. Tana ganinsa ta cire wayar tana zare idanu. “Ke ashe baki da hankah? Da izinin uban wa kika je kika yi hira da ‘…