RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Sultan nayi kuskure mai girma! Ban barka ka samu kyakkyawar zama da Nasreen ba.” Dukkansu suka dube shi cikin rashin fahimta. “Sultan Nasreen matarka ce, matarka ce aka sace – ta. Na hada aurenku domin ganin ka sami daman rike amanar Saudat da kyau! Yau sai gashi ka rasa matarka. Ban sani ba ko kasheta akayi, idan kuwa tana da rai za ta yi ta yawo da igiyar aurenka akanta.” Ba Umma ba, hatta Sultan sai da maganar tayi masa girma. Damuwarsa ta sake ninkuwa. Daman Nasreen matarsa ce? Da , yasan matarsa ce me Zai sa jiya/ya gaya mata irin wannan kalaman? Rintse ido yayi yana jin | kamar mahaifinsa bai kyauta masa ba. Umma kuwa tunani take yi a zuciyarta me yasa batasa a kashe Nasreen ba kawai ta huta? A fusace ta mike, “Allah na gode maka da aka saceta. Ashe so ta yi ta kanainaiye min gida? Kana nufin Nasreen ita ce matar Sultan? Amma dai Alhaji ka gama cutata. Da inga wannan baKa…