RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO
RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.” Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.” ZAMU TASHI Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta …