NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH  BOOK 2  CHAPTER  7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI                    Www.bankinhausanovels.com.ng  MUN TSAYA  Alh. ya shige bandaki shi kuma ya nemi kujera ya zauna ya ci magani yana ta faman muzurai da saKe-sake har Alh. ya fito daga bandakin ya hakimce a kujera cikin kalar nasa « nuna bacin rai “Ba na so in ce daga ina kake Adamu, don kar in ji amsar rainin hankali ta janyo in tashi in kashe ka da mari” Adamu yayi fuska iyakar fuska, : “Ni dai namiji ne, bare a ce yawon duniya _ na tafi” . Mamaki ya cika Alh. wannan fa shi ake kira Karfin hali wai barawo da sallama, daga bisani kuma sai ransa ya baci ya Kura wa ido Adamu cikin bacin rai. Adamu ya muskuta ya sake muskutawa yana wani basarwa, – . “Wallahi fashina aka yi” – .Alh. ya jima bai tanka ba saboda tsabar haushi ya ma rasa me zai cewa Adamu, dama abinda ya guda kenan, ya san Adamu zai iya * zuwa masa da rainin hankalin da zai tunzura. shi, ilai kuwa. Sai faman kokawar hadiye fishinsa -yake, har ya samu ya hadiyu, ya sassauta…