NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
NA SHIGA ALJANNAH  BOOK 2  CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA  Hankalin Adamu sam bai kwanta ba, tsoron ko kashe matar ubansa da Salmanu yake ta kirarin yi ya tafi cikawa ya kada cikin Adamu ainun, kawai sai yayi saurin rufe dakinsa ya tafi cikin gida wajen mahaifiyarsa _ hira, abinda ya jima bai yi ba musamman a lokaci? irin wannan, shi manufarsa, idan ma wata aika-aikar Salmanu ya je yayi ko an kama Salmanun idan aka hado da shi zai iya samun shaidar cewa ai dai-dai wanna lokacin yana’ cikin gidansu kusa da gyatumarsa, musamman dayake gidan nasu Kafa bata daukewa da masu siyen goro, ko wani bai gan shi ba wani zai gan shi tare da mahaifiyar — tasa. Salmanu na zaune a dakalin Kofar gidansu. Adamu cikin shigarsa ta Basaja_. wadda idan ba farin sani kayi masa ba daga kallo daya ba zaka shaida shi ba. – Duk da ba aikin kirki yake shirin yi ba cikin nutsuwarsa yake, lokaci-lokaci yana kallon hanya har tsawon fiye da mintuna talatin. Allah ya tai…