NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CH
NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Bayan sun dawo. suka wuce cikin gida Salmanu ya gai da Hajiya, suka dan jima tare da ita suna hira tana Kara yi musu nasiha kamar. ‘yadda ta saba, ta yau har ta fi ta kullum kasancewar tana cikin firgicin halin da Adamu yake shirin fadawa. – Bayan sun dawo dakin Adamu suka ci abinci suka cigaba da hira. Wai me yasa na ga Hajiya a firgice? Ina fatan ba zuwana ba ne?” Salmanu ya tambaya. “Kan zargin na je wajen Malam-na-Allah – ne , -Adamu ya amsa. ZAMU TASHI Tana da gaskiya, kuma da na san haka ne, da na kwantar mata da hankali na fada mata gaskiya “Gara da baka sani ba din, yanzu mu je ga abinda ya kawo ka” Salmanu ya gyara zama cikin jin kumari da nishadi, “Faduwa ce fa ta zo daidai da zama, hanyar neman kudi da samunsu cikin sassaukar hanya na kawo mana, dabararmu ce kawai zata yi aiki..” “Kai da ka ce baka son ganin Kato na jiran kudi a huce?” Adamu ya fada cikin gwasalewa. S…