MY BESTIE'S HUSBAND CHAPTER 2 BY REALFAUZAHTASIU
MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 2 BY REALFAUZAHTASIU Www.bankinhausanovels.com.ng _____________________________ _____________________________ Girgiza Kai Rafi’ah tayi tace “Aa Ni’imah mijinki azzalumine bashida adalci baison me sonsa ba meyesa laifin wani zai shafi wani….” Katseta tayi tace “naji Rafi’ah nidai ki taimakeni kije don darajar qauna da aminta kinji” ajiyar zuciya tayi jikinta ya qara sanyi tace “shikenan zanyi qoqari bari zance da Ammi zanzo gurinki asibiti duk yanda mukayi zakiji” ajiye wayar tayi ta fara kaiwa da komowa a dakin zuciyarta cunkushe da tsoro yanzu ita ya zaayi ta taka taje gidan Ja’afar Wakil da wanne irin yanayi zai karbeta? Tambayar da takeyiwa kanta ta kasa samun amsa kenan daqyar ta iya sawa kanta juriya ta dauki doguwar rigarta ta zura tayi rolling mayafin ta dauki takalmi da wayarta da key din motar Ammi ta fice daga dakin ta nufi dakin ammi tana bisa sallaya ta zauna bayan ta idar da sallar ta dubi yar tata tace “ina zaki?” Sunkuyar dakai …