ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir Na ce, “Kin bata wayonki Ummi, wallahi kika aure shi za ki kwashi kashinki a hannu. Na rantse mai hali…….” “Baya fasa halinsa fa Fa’izah!” Ta karasa tana min dariyar tura haushi. Ta kuwa tura din. Ta ci gaba da cewa, “A ganina wannan ba damuwar ki ba ce tunda dai ba ke za ki zauna min dashi ba, bai shafe ki ba kowacce irin rayuwa zamu yi ni da Ya Fa’iz, tunda abin sa-kai-ne. Ina SON SHI HAKA! Shine kadai ya tara dukkan abubuwan da nake so ga Da namiji, har ma ya zarta. Kafin a samu namijin da ya tara sura da ‘attributes’ din duk da ‘ya mace ke so irin Fa’iz za a jima Fa’izah. Don haka Fa’izah a yau ina mai farin cikin shaida miki cewa, ina son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!” Sai na ce, “Allah ya ganar dake Ummi. Kin riga kin yi nisa ba za ki ji kiran ba. Allah ya shirye ki, ya ganar i O < dake makiyinka baya taba rikidewa ya dawo masoyinka, ‘no matter what… sai in ya ga kiyayyar tasa ba mai ci ba “wai ke sai kira kike FA’IZ MAKI…