ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir BOOK 1 KARSHE amince ayi aurenmu da zarar kin yl graduating?” Na langanar da kai na ce, “Haba Yaya Aliyu”. Ya yi murmushi ya zauna, nima na zauna, muka dubi juna, sai muka sa dariya a tare. “Ke fa shu’uma ce Fa’izah, in mun yi aure zan sha wahalarki”’. Na kau da zancen cikin jin kunya da cewa, “Zanirah fa tana ciki Yaya Aliyu in kirawo ta?” Ya ce, “In mata me? Ke, ina fa da abin yi, za ki bani amsata ne ko kuwa?”’ Na yi rau-rau da ido kamar mai shirin kuka na ce, “Haka ake ba da amsar Yaya Aliyu kamar a fagen fama? Don Allah ka yi hakuri na amsa duka laifuffukana”’. Ya saki rai ya ce, “Ok!” Na koma kicin na kawo mishi wani ruwan, har da cake da dambun naman kaza ya soma ci yana hararata ina share fasasshen kofin tangaram ina murmushi. Na kammala na koma daki na dauko takarda na dunkule a hannuna na fito. Zuwa lokacin Yaya ya gama, na ce, “To Yaya Aliyu rufe idonka’”. Ya mai da manyan idanunshi ya lumshe zarazaran gassun girarsa. Ya b…