ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir Na yi iyaka_ tunanina amma hankalina bai bani ba. Baban ku ma ya yi tambayar duniyar nan amma ta kafe sai ana saura kwana uku daurin auren sannan kowa zai j1”.  Na ce, “Kai wannan tsohuwa da rigima take, ke Zanirah to mene ne abin kuka? Muma muna tafe, kin sani dai ko ba yanzu ba mawuyaci ne Hajjah ta kyale ki zuwa jami’a da shekaru kusa da ashirin, kai Hajjah ta yi dai-dai….”  Zanirah ta taso kamar za ta make ni, ko me ta tuna? Sai ta juya ta yi bed room din Mama tana sharbar kuka wiwi kamar ranta zai fita.  Ni dai Allah-Allah nake karfe uku ta yi na bar gidan zuwa Zaria kafin Yaya Aliyu ya dawo ya taddani, duk da Aunty Hauwa ta ce in bi umarnin makaranta duka gidajen biyu ba zan iya zama ba, can Ummi mun yi fada, nan Yaya Aliyu zai tirke ni. Ya kasa ganewa cewa nauyinsa da girmansa da nake gani ba zai barni in ba shi amsar  wasikarsa ba. Na yi kokarin hakan amma na kasa.  Karfe ukun na yi na dauki jakata na yafa mayafi, na yiwa Mama sallam…